No menu items!

Sample Page Title

Date:

Tinubu ya naɗa Patricia Manko a matsayin sabuwar shugabar jami’ar Yakubu Gowon da ke Abuja

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da yin wani gagarumin garanbawul a jami’o’in gwamnatin tarayyar kasar da dama, ciki har da Jami’ar Abuja, da yanzu aka sauya wa suna zuwa Jami’ar Yakubu Gowon.

Da take tabbatar da sauye-sauyen, sanarwar da mashawarcin shugaban Najeriyar na musamman a kan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, yace sauye-sauyen sun fara aiki ne nan take.

Shugaba Tinubu ya rushe majalisar gudanarwar jami’ar tare da sauke Farfesa Aisha Sani Maikudi daga kan mukaminta na shugabancin Jami’ar Yakubu Gowon.

KU KUMA KARANTA:Wasu malamai sun yi zargin rashin bin ƙa’ida wajen naɗa shugabar jami’ar Abuja

An kuma nada shugaban majalisar gudanarwar jami’ar aikin gona ta Makurdi na yanzu, Sanata Lanretejuoso a matsayin shugaban majalisar gudanarwar jami’ar ta Yakubu Gowon.

Sanata Joy Emordi wanda ke zama shugabar majalisar gudanarwar jami’ar Alvan Ikoku za ta maye gurbinsa a jami’ar aikin gona ta Makurdi.

Shugaba Tinubu ya kuma nada Farfesa Lar Patricia Manko a matsayin shugabar Jami’ar Yakubu Gowon ta riko tsawon wa’adin watanni 6.

Ba za ta cancanci shiga takarar zama cikakkiyar shugabar jami’ar ba idan wa’adin ta ya kare.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...