Hatsarin mota ya kashe mutane 4 tare da jikkata wasu 13 a Neja

0
10
Hatsarin mota ya kashe mutane 4 tare da jikkata wasu 13 a Neja

 

Hatsarin mota ya kashe mutane 4 tare da jikkata wasu 13 a Neja

Wani mummunan hatsarin mota akan babbar hanyar agaie zuwa Lapai ta jihar Neja ya hallaka mutane 4 tare da jikkata wasu 13.

Mummunan hatsarin, wanda ya afku a kusa da Al’Farma International School da ke karamar hukumar Agaie, ya faru ne sakamakon taho mu gamar da wasu tireloli 3 suka yi, ciki har da wata mai safarar dabbobi.

Sanarwar da babban daraktan hukumar agajin gaggawa ta jihar Neja (nsema), Abdullahi Baba-Arah ya fitar, tace mummunan obataki ne ya haddasa hatsarin.

KU KUMA KARANTA:Hatsarin mota a Yobe ya ci rayukan mutane 12

Karfin taho mu gamar yayi matukar yin muni, inda nan take ya sabbaba mutuwar mutane 2 a wurin da hatsarin ya afku, yayin da sauran suka rasu a asibiti sakamakon raunukan da suka samu.

Baya ga mutuwar mutane, hatsarin ya kuma sabbaba mutuwar kimanin shanu 15 da awaki fiye da 20.

Nan take aka garzya da wadanda hatsarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Agaie inda suke samun kulawar likitoci.

Leave a Reply