An fara bawa mazauna Kano bashin man fetur
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Wani kamfani mai suna BloomData Limited ya ƙaddamar da wani shiri mai taken BloomFuel Service don sayar da man fetur da dizel bashi ga masu ƙananan sana’o’i a jihar Kano.
Da ya ke jawabi wajen ƙaddamar da shirin, shugaban kamfanin, Ja’afar Gambo ya ce an kirkiro da shirin ne don saukaka wa masu ƙananan sana’o’i, musamman masu motoci da baburan haya.
KU KUMA KARANTA:Abin da ya sa aka dakatar da mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars
A cewar sa, yanzu shirin ya fara da masu motoci da baburan haya, ta hannun ƙungiyoyin su, inda za su rika zuwa gidan man AA Rano su sayi mai a kan bashi sannan su biya cikin awanni 24.
Ya ce tuni an yi wa masu ababen hawa na haya guda 300 rijista, inda a yanzu haka akwai wadanda su ka cike fom sama da mutum 900.
Ya ce idan shirin ya dore, za a samu bunƙasar arziki da wata kuma a cewar sa, “gwamnati za ta samu ƙarin kuɗaɗen shiga,”