No menu items!

Sample Page Title

Date:

An kammala shirin taron ‘Qur’an Convention’ a Abuja

Da alamun shirye-shiryen gudanar da babban taron hafizan Alkur’ani Mai Girma sun kankama a Abuja, inda manyan allunan sanarwa kan taron su ka bayyana a muhimman sassan birnin.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da a ke ci gaba da muhawara kan dalilan taron da ya ke irin sa na farko a Abuja.

Murtala Garba na daga fitattu a matasan da ke cewa taron zai kara kawo hadin kai a tsakanin makarnta na sassa daban-daban na Najeriya.

Taron dai wanda zai gudana karkashin majalisar koli ta Islama karkashin mai alfarma Sarkin musulumi Muhammad Sa’ad Abubakar na da zummar tara dubban alarammomi don su yi karatun ruwayoyin, kuma daga dukkan kungiyoyin Islama da su ka hada da sufaye, salafawa da sauran su.

KU KUMA KARANTA:Sarkin yaƙin Zazzau Rilwanu Pate ya rasu

Na tambayi shugaban kwamitin fatawa na majalisar kolin Sheikh Shariff Ibrahim Saleh kan muhimmanci ko ingancin taro na karatun Alkur’ani sai ya ce, “..karatun kur’ani saboda a samu nasara a wurin Allah kan hadin kai ko sauran su, shari’a ba ta hana ba, amma kuma ba ita ce aiki kurum ba, ya kamata duk mutane masu zama wuri daya su hada kan su don su amfani kan su da jama’ar da su ke tare da su. Saboda haka mu na so wannan sunna ta rayu har abada”

Duk da a na sa ran shugaba Tinubu zai halarci taron ranar 22 ga watan nan na Febreru, amma kai tsaye ba wani bayani daga wani jami’in gwamnati da ya alakanta abun da siyasa ko bukatar neman goyon bayan jama’a ga zabe mai zuwa a 2027 da ke da nisa daga yanzu; da hakan ya saba da zarge-zarge a yanar gizo.

Dattijon ‘yan siyasar arewa, Injiniya Kailani Muhammad, ya ce taron zai karfafa karatun tsangaya da gwamnati ta fara maida hankali a kai a zamanin tsohon shugaba Jonathan ”a lokacin shugaba Jonathan ya kawo maganar tsangaya da za a taimaka mu su sai mu ka samu akasi a lokacin Buhari, aka soke tafiyar tsangaya. Yanzu lokaci ya yi da za a dawo da ita a kai mu su makarantar boko”

Kwamitin shirya taron da ya hada da manyan malaman Islama ya bude dandalin yanar gizo don samar da bayanai ga masu niyyar halartar taron.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...