No menu items!

Sample Page Title

Date:

Isra’ila ta buɗe wa Falasɗinawa hanyar komawa arewacin Gaza

A ranar Litinin ne dubu dubatan Falasdinawa ke tururuwa akan babbar hanyar zuwa arewacin Gaza, suna murnar komawa gidajensu bayan shafe watanni a matsugunan wucin gadi saidai suna fargabar abinda zai saura na gidajen daga baraguzan gine-ginen da aka yiwa ruwan bama-bamai.

Komawar tasu, wacce aka jinkirta a karshen mako, ta cigaba bayan da kungiyar Hamas ta amince ta mika Yahudawan da take garkuwa dasu wani lokaci a makon da muke ciki sannan dakarun Isra’ila sun fara janyewa daga babbar hanyar data ratsa zirin a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin da ake shafe watanni 15 ana gwabzawa.

A Isra’ila, iyalai na jira cikin kaguwa domin samun labarin makomar; yan uwansu.

A kan hanyar dake gabar tekun Meditareniya, dandazon jama’a wasu na dauke da jarirai a hannu ko daurin kaya a kafadunsu, sun nausa zuwa yankin arewa a kafa.

KU KUMA KARANTA:Paparoma Francis ya yi Alla-wadai da matakan Sojin Isra’ila a Gaza

Shaidun gani da ido sun ce tawagar farko ta isa birnin Gaza sanyin safiya bayan da aka bude mashigar farko dake yankin tsakiyar gaza da misalin karfe 7 na safe agogon GMT. An sake bude wata mashigar bayan sa’o’i 3, inda aka kyale ababen hawa su wuce.

“Zuciyata na dakan uku-uku, na zaci ba zan taba dawowa ba,” a cewar Osama, wani ma’aikacin hukuma mai shekaru 50 kuma uba ga ‘ya’ya 5sa’ilin daya isa Birnin Gaza.

“Ko yarjejeniyar tsagaita wutar tayi nasara ko akasin hakan, baza mu sake barin birnin Gaza ko yankin arewaci ba, ko kuwa da Isra’ila zata aikewa kowane guda daga cikinmu tankar yaki, ba zamu sake barin gidajenmu ba.”

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...