Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta yi bikin yaye ɗalibai kashi na 44
Daga Idris Umar, Zariya
Yau asabar Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, tayi bikin yaye ɗalibanta karo na 44.
Mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ya kasance cikin muhimman mutanen da suka halarci wannan biki mai muhimmanci.
Jami’ar ta yaye Dalubai Dubu Ashirin da ɗaya ɗa ɗari tara da hamsin da biyu (21,952) a mabanbantan ɓangarorin Ilimi dake harabar jami’ar.
KU KUMA KARANTA:NAFDAC ta lalata kayayyakin jabu na Naira biliyan 1.3 a Abuja
Daga cikin muhimman mutanen da suka halarci wannan biki sun hada da mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar III da Basarake Nnaemeka Alfred Ugochukwu Obi na Onitsha Uban Jami’an sai Alhaji Mahmud Yayale Ahmed Ajiyan Katagum tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Majalisar Jami’an Ahmadu Bello sai Karamar Hukumar Ilimi Dokta Suwaiba Sa’ad Ahmad da Farfesa Muhammadu Sani Bello Mainan Zazzau, waɗanda suka wakilci Gwamnantin Tarayya da na Jihar Kaduna.
Jami’ar dai ta karrama fittacen malamin Addinin Musulunci Sheikh Ibrahim Sharif Hassan Al-Hussaini da Babban Digiri kan Shari’a.
Haka nan a nan gaba Jami’ar zata Karamma Dokta Ngozi Okonjo-Iweala wanda bata sami daman halartan bikin ba da nata babban Digiri a fannin Kimiyya.
An gabatar da muƙaloli daban daban masu nuni da nasara da ƙalubale da jam’iyar ke fuskanta.
Anyi taron lafiya an gama lafiya.