No menu items!

Sample Page Title

Date:

‘Yansanda sun fake da barazanar tsaro ne kawai don su hana Maulidin Tijjaniyya – Gwamnatin Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnatin Jihar Kano ta zargi ‘yasanda da ƙoƙarin hana taron addini na Ɗariƙar Tijjaniyya na shekara-shekara a jihar, inda ta ƙaryata cewa akwai barazanar tsaro a jihar kamar yadda rundunar ‘yansanda ta sanar a ranar juma’a a jihar.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a Fadar Sarkin Kano a ranar Juma’a, Kwamishinan yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comr, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya musanta gargadin da ‘yan sanda suka fitar tun da fari.

KU KUMA KARANTA:Gwamna Kano ya jinjinawa rundunar ‘yansanda kan tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano

Waiya ya ce rundunar ƴansanda kawai ta fake da barazanar tsaro ne don ta hana gudanar da taron Mauludin na Tijjaniyya na kasa, wanda ya ce an kwashe kusan shekaru 40 ana gudanar da shi.

Kwamishinan ya bayyana cewa, duk da matakin da ƴansanda suka dauka, Mauludin zai gudana kamar yadda aka tsara a filin wasa na Kofar Mata, yana mai tabbatar wa wadanda ke son halarta cewa gwamnatin jihar ba za ta bari a samu wata matsala ba.

Toni dai Jihar Kano tayi cika kwari da miliyoyin jama’a da sassan Jihar da wasu daga cikin makwabtan kasashen Nijeriya domin gudanar da taron, a gefe guda cikin daren tawagar Gwamnatin Kano ta ziyarci babban filin wasa na Muhammad Sani Abacha da ke kofar mata inda a nan ne za’a gudanar da taron.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...