Motar dakon mai ta kama da wuta a Neja, ta kashe mutane 80

0
18
Motar dakon mai ta kama da wuta a Neja, ta kashe mutane 80

Motar dakon mai ta kama da wuta a Neja, ta kashe mutane 80

Aƙalla mutane 80 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a arewacin Najeriya a ranar Asabar bayan da wata motar dakon mai ta kife, ta kuma zubar da mai da kafin daga bisani ta fashe, a cewar hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC).

Hatsarin da ya afku a jihar Neja ya biyo bayan wata fashewar makamancin haka a jihar Jigawa a watan Oktoban da ya gabata wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 147, daya daga cikin bala’o’i mafi muni a kasar da ta fi yawan al’umma a Afirka.

Kumar Tsukwam, kwamandan hukumar FRSC shiyyar jihar Neja, ya ce akasarin wadanda abin ya rutsa da su talakawa ne mazauna yankin da suka yi gaggawar dibar man fetur da ya zube bayan motar ta kife.

KU KUMA KARANTA:Faɗuwar tankar mai a Jigawa, mutane 94 sun ƙone ƙurmus, 50 sun samu raunuka

“Mutane da yawa sun taru domin diban mai duk da kokarin da aka yi na hana su,” inji Tsukwam a cikin wata sanarwa.

“Kwatsam, sai motar tankar ta kama wuta, ta kuma kona wata motar dakon mai, ya zuwa yanzu an kwashe gawarwaki 60 da aka gano a wurin.”

Tsukwam ya ce jami’an kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar.

Irin wadannan hadurran dai sun zama ruwan dare a kasar da ta fi kowacce kasa hako mai a nahiyar Afirka, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a kasar da ke fama da matsalar tsadar rayuwa na tarihi.

Farashin man fetur a Najeriya ya haura sama da kashi 400 tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya janye tallafin mai da aka kwashe tsawon shekaru ana cin moriyarsa a lokacin da ya hau mulki a watan Mayun 2023.

Leave a Reply