Kwararowar ‘yan bindiga daga yankin Sahel, na haddasa ƙaruwar ayyukan ta’addanci a Najeriya – Rundunar Tsaro

0
21
Kwararowar 'yan bindiga daga yankin Sahel, na haddasa ƙaruwar ayyukan ta'addanci a Najeriya - Rundunar Tsaro

Kwararowar ‘yan bindiga daga yankin Sahel, na haddasa ƙaruwar ayyukan ta’addanci a Najeriya – Rundunar Tsaro

Hedikwatar rundunar tsaron Najeriya ta ce tuttuɗowar ‘yan ta’adda daga yankin Sahel yana daɗa haifar da ƙaruwar hare-haren ta’addanci a Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Rundunar tsaron Najeriya ta yaba da cafke Simon Ekpa

A wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar tsaron kasa da ke Abuja, daraktan sashen tattara bayanai kan fafatawa da sojojin Najeriya su ke yi, Manjo Janar Edward Buba, ya ce a ‘yan kwanakin bayan nan, ana samun karuwar hare haren ta’addanci.

Manjo Janar Buba, ya ce ‘yan bindigar su na kwararowa ta wurare irin su Kareto, Wajiroko, Chibok, Gwoza da sabon gari a jihar Barno, sai Gudu, Illela, Sabon Birni da sauran wurare a yankin arewa maso yammacin Najeriya. Daraktan ya ce ana samun ta’azarar hare haren ne saboda yadda mayakan na ketare suke samun goyon bayan abokan aika aikarsu wadanda suke tsegunta masu kai komon sojoji.

Ya ce ko da yake sojoji suna fuskantar dan koma baya a wasu bangarori, suna samun kwarin gwiwar karya lagon abokan gaba.

Da yake tsokaci akan wannan batu, shugaban kamfanin tsaro na BEACON INTEL Dr. Kabiru Adamu, ya ce bisa yadda bincikensu ya nuna, akwai alamun bakin ‘yan ta’adda na tuttudowa cikin Najeriya kuma abin da ya haddasa hakan shi ne tsamin dangantaka da ke tsakanin Najeriya da makwabciyar ta Nijar da kuma fatattakar ‘yan ta’adda da kasar Tchadi ta yi daga kasarta.

Leave a Reply