‘Yansanda sun gurfanar da Shamsiyya a kotu bisa zargin satar wayoyi a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Rundunar ‘yansanda a jihar Kano ta ce ta gurfanar da wasu matasa da ta kama a jihar, gaban kotu, bisa zargin su da satar wayoyi.
A makon da ya gabata ne rundunar ta sanar da kamen matasan bayan ƙorafe-ƙorafe da ta ce ta samu daga mutane da dama.
Wata majiya ta rawaito cewa mai magana da yawun rundunar ‘yansandan a jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an gurfanar da matasan, waɗanda suka haɗa da maza huɗu da mace ɗaya, wadda ake kira Shamsiyya.
SP Abdullahi Kiyawa ya kuma ce ‘yansanda sun kama ƙarin wasu mutum huɗu da suke da alaƙa da tawagar.
KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Abuja sun kama sojoji na jabu tare da motoci 296 na sata
Kiyawa ya ce mutum 86 ne suka kai ƙarar waɗanda ake zargi, wanda hakan ya sa Kwamishinan ‘yansandan jihar, Salman Dogo Garba ya kafa runduna ta musamman domin bin diddigi, inda suka samu nasarar kama waɗanda ake zargi, kuma aka ƙwato wasu wayoyin.
Lamarin ƙwace da satar waya a Kano, jiha mafi yawan al’umma a arewacin Najeriya, babbar matsala ce da ke addabar al’umma.
An samu rahotanni da dama na yadda masu satar waya kan kai hari tare da illata mutane a lokacin da suke yunƙurin aiwatar da ɓarnar a jihar ta Kano.