Ba zan taimaki gwamnatin Tinubu ba – Sarkin Kano Sanusi

0
73
Ba zan taimaki gwamnatin Tinubu ba - Sarkin Kano Sanusi

Ba zan taimaki gwamnatin Tinubu ba – Sarkin Kano Sanusi

Daga Ibraheem El-Tafseer

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce ba zai taimaki wannan gwamnatin ta Shugaba Tinubu ba ko da da shawarwari ne.

Sarkin ya bayyana haka ne a wajen taron tunawa da fitaccen lauyan nan ɗan gwagwarmaya na Najeriya, Chief Gani Fawehinmi karo na 21 a birnin Ikko, Legas.

Ya ce, zai iya yin bayani a kan ‘yan wasu abubuwa game da abubuwan da Najeriya ke ciki da hasashen abin da zai iya faruwa da kuma yadda za a iya kaucewa hakan, to amma ya ce ba zai yi hakan ba, domin idan ya yi hakan zai taimake su (gwamnatin Tinubu), shi kuma ya ce ba zai taimake su ba.

Sarkin ya ce, ya yanke shawara cewa ba zai yi magana a kan tattalin arziƙi ko sauye-sauyen da gwamnatin ke yi ba ko ma ya yi bayani a kan komai, ”saboda idan na yi bayani hakan, za taimaki gwamnatin, to amma ba na son in taimaki gwamnatin nan da abin da za ta ci gaba.”

KU KUMA KARANTA: 2025: Mu haɗa kai mu ci gaba da tafiya domin gina ƙasar nan ; Shugaba Tinubu

Ya kara da cewa, ”Abokanaina ne, to amma idan ba sa yin abu kamar abokanai, ni ma ba zan dauke su kamar abokanai ba.”

”Ba ma su da mutane masu kima da za su zo su yi bayanin abin da suke yi ba. Ba zan taimaka ba,” in ji shi.

Leave a Reply