An naɗa sabon shugaban Jami’ar jihar Yobe na riƙo
Daga Ibraheem El-Tafseer
Majalisar gudanarwar jami’ar jihar Yobe dake Damaturu, ta amince da naɗin Farfesa Bukar Jamri a matsayin shugaban jami’ar na riƙo.
Daraktar yaɗa labarai ta jami’ar, Hajiya Uwani-Mamuda ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Damaturu, ranar Laraba, cewa naɗin zai fara aiki ne daga ranar 13 ga watan Fabrairu.
A cewarta, naɗin Jamri ya biyo bayan cikar wa’adin Farfesa Mala Daura, shugaban Jami’ar na yanzu.
Ta ce majalisar ta kuma amince da naɗin Malam Garba Girgir, a matsayin rajistaran jami’ar na riƙo, daga ranar 15 ga watan Janairu.
KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya yi wa babban hafsan Sojin Ƙasa na riƙo ƙarin girma
Daraktan ta ce an amince da naɗin su biyun ne a wani zama na musamman da majalisar ta yi ranar Laraba.
Jamri shi ne Mataimakin shugaban jami’ar ɓangaren gudanarwa.