Sojoji a Zamfara sun tarwatsa sansanin Bello Turji, sun kashe ‘yan ta’adda 25

0
31
Sojoji a Zamfara sun tarwatsa sansanin Bello Turji, sun kashe 'yan ta'adda 25

Sojoji a Zamfara sun tarwatsa sansanin Bello Turji, sun kashe ‘yan ta’adda 25

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe ‘yan ta’adda 25 da jikkata 18 da tarwatsa maɓoyarsu a Jihar Zamfara.

Dakarun Operation Fansan Yamma ne suka yi wannan aikin a yankin Fakai na Ƙaramar Hukumar Shinkafi yayin wani samame da suka kai a ranar 10 ga watan Janairun 2025.

A sanarwar da mai magana da yawun dakarun na Operation Fansan Yamma Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, daga cikin sansanonin ‘yan ta’addan da suka kai wa farmaki har da na Bello Turji.

“Dakarun a wani samame da suka kai da taimakon sojojin sama na Operation Fansan Yamma, sun tarwatsa wasu sansanonin ‘yan ta’adda a yankin Fakai.

“Wasu daga cikin sansanonin da aka tarwatsa sun haɗa da na Bello Turji da Malam Ila inda a nan ‘yan bindigan suka kashe fiye da ‘yan ta’adda 25 da jikkata 18, inda hakan ya jawo koma baya ga ‘yan ta’addan,” in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: Rundunar sojojin saman Najeriya ta ƙwato bindigogi dubu 8 daga hannun ;yan taadda

Haka kuma sojojin sun ce mutum bakwai da aka yi garkuwa da su sun tsere a daidai lokacin da suke kai samamen.

Jihar Zamfara na daga cikin yankunan da ‘yan bindiga ke kai wa hare-hare tare da garkuwa da mutane a arewacin Najeriya.

Sai dai hukumomin ƙasar na cewa suna samun nasara a yaƙi da suke yi da ta’addanci a ƙasar.

Leave a Reply