Kotu ta yanke hukuncin rataye wani mutum mai laifin fashi da makami 

0
31
Kotu ta yanke hukuncin rataye wani mutum mai laifin fashi da makami 

Kotu ta yanke hukuncin rataye wani mutum mai laifin fashi da makami

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Babbar Kotun jahar Kano mai lamba 11 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Nasir Saminu, ta zartas da hukuncin kisa akan wani mutum wanda kotun ta samu da laifin fashi da Makami.

Mutumin mai suna Abdurrahman Yakubu mazaunin karamar hukumar Bele dake jihar Nassarawa, kotun ta same shi ne da laifin yi wa mutane da yawa fashi da makami ta hanyar amfani da muggan Makamai.

Cikin mutanen da mutumin ya yi wa fashin hadda wata mata mai suna Barrister Hajara Lawal Ahmad, wadda ya yi wa fashin mota da kuma Kuɗi.

KU KUMA KARANTA: Za a rataye wani ɗan aiki da ya kashe tsohuwa, da yarta

Yayin da ya ke zartas da hukuncin mai Shari’a Saminu ya ayyana cewar, Kotun ta gamsu da shaidun da lauyan gwamnati Barrister Umar Yakubu ya gabatar, inda kotun ta yi watsi da shaidar da Abdurrahaman ya bayar domin kare kansa.

Kotun ta kuma bayyana cewar ta gamsu da muggan makaman da aka samu a hannun Abdurrahan haramtattu ne, kuma ana tasarifi da su ta haramtacciyar hanya dan haka kotun ta yi umarnin a kashe shi ta hanyar rataya.

Wakilin Neptune Prime a Kano, Jamilu Lawan Yakasai ya ruwaito cewa, bayan yanke hukuncin mai Shari’a Saminu ya yi masa addu’ar cikawa da kyau.

Leave a Reply