Rashin Ruwan Sha: Al’ummar garin Kanwa da ke Kano suna shan ruwan da dabbobi ke sha

0
8
Rashin Ruwan Sha: Al'ummar garin Kanwa da ke Kano suna shan ruwan da dabbobi ke sha

Rashin Ruwan Sha: Al’ummar garin Kanwa da ke Kano suna shan ruwan da dabbobi ke sha

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Ruwa shin abokin rayuwa, hakan yasa masana kiwon lafiya ke faɗakar da al’umma amfani da tsaftattacen ruwan sha domin samun ingantacciyar lafiya.

Sai dai wasu shan ruwa mai tsafta ya zamar musu wahala, sakamakon rashin samunsa a inda suke rayuwa, musamman al’ummar karkara,

Garin kanwa yana daga yankin ƙaramar hukumar dawakin kudu a Jihar Kano, al’ummar wannan yankin na fama da barazanar samun wadatacciyar lafiya, sakamakon amfani da ruwan wani kogi wanda ke a gefen garin, wannan ruwa ya kasance shi suke sha, suyi amfani da shi wajen girka abinci da dai sauransu, kamar yadda wani da muka samu ya shiga cikin ruwan ya sanya jarka yana ɗiba yake bayyana mana.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta karɓo bashi daga Faransa domin aikin ruwan sha

Inda yace dabobbinsu suma suna shiga wannan ruwa su sha, munyi ƙoƙarin ganawa da shugaban wannan yanki sai dai munyi sabanin haɗuwa da shi, za mu ci gaba da bibiya domin jin koyasan halin da wannan yankin yake ciki? Idan ya sani wanne koƙari yake wajen kawo wa al’ummar wannan yankin agajin gaggawa, kucigaba da bibiyarmu domin jin wacce amsa wannan Shugaban karamar hukuma zai bamu.

Sai dai a wata zantawa da sabon Kwamishinan ruwa na jihar Kano da manema labarai a satin daya gabata Hon. Umar Haruna Doguwa yace hukumarsa ta ɗauki alƙawarin nan da watanni uku masu zuwa ruwa zai wadata a Jihar Kano gaba-ɗaya, abun jira a gani anan shine lokaci.

Leave a Reply