Hukumar NFF ta naɗa Éric Chelle a matsayin sabon kocin Super Eagles
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) ta naɗa Éric Sékou Chelle a matsayin sabon kocin tawagar Super Eagles.
Naɗin na Chelle ya samu amincewa bayan taron da NFF ta gudanar a Abuja a ranar 2 ga watan Janairu, 2025, sannan aka kammala amincewa da shi a ranar 7 ga watan Janairu, 2025.
Chelle, wanda ke da shekaru 47, tsohon kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Mali, ya jagoranci kulab da dama kamar GS Consolat, FC Martigues, Boulogne, da MC Oran.
A lokacin da yake wasa, Chelle ya buga ƙwallo a kulab ɗin ƙasar Faransa irin su Martigues, Valenciennes, da Lens.
An haifi Chelle a ƙasar Côte d’Ivoire, daga mahaifi ɗan asalin Faransa da mahaifiya ‘yar ƙasar Mali.
KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar Manchester United ta sallami kocinta
Ya zaɓi yin wasa da Mali, inda ya taka leda a wasannin ƙasa guda biyar kafin ya yi ritaya daga wasannin ƙwallo.
Chelle ya jagoranci tawagar Mali daga 2022 zuwa 2024, inda ya kai su zuwa matakin kwata-fayinal a gasar Cin Kofin Afirka ta 2023 (AFCON).
Chelle ya karbi shugabancin Super Eagles bayan Finidi George ya murabus saboda rashin nasara a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026.
Aikin Chelle na farko zai zama jagorantar Najeriya zuwa samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026.