Sojoji sun ƙwace litar mai 90,000 da lalata haramtattun matatun mai guda 20

0
26
Sojoji sun ƙwace litar mai 90,000 da lalata haramtattun matatun mai guda 20

Sojoji sun ƙwace litar mai 90,000 da lalata haramtattun matatun mai guda 20

Dakarun runduna ta 6 ta sojojin Najeriya sun lalata haramtattun wuraren tace man fetur 20, sannan sun kwace lita dubu 90,000 na mai da aka sace, tare da cafke wasu mutane takwas da ake zargi a yankin Niger Delta.

Rundunar ta bayyana cewa ta samu wannan nasarar ce a wani samame da ta kai tare da hadin gwiwar takwarorinsu a fannin tsaro a jihohin Rivers da Bayelsa da Akwa Ibom da kuma Delta.

Mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na runduna ta 6, Laftanar Kanar Jonah Danjuma ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Port harcourt a ranar Lahadin nan.

Laftanal Kanal Danjuma ya ce an kai samamen ne a jihohin hudu tsakanin ranakun 23 zuwa 29 ga watan Disamban 2024.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Rundunar ta 6 ta sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun ci gaba da kai hare-hare kan masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a yankin Neja Delta.

Danjuna ya ci ba da cewa “Wannan yunƙurin ya kai ga tarwatsa haramtattun matatun matatu guda 20, sannan aka kama wasu mutane takwas da ake zargin barayin mai ne, da kuma lalata jiragen ruwa 21 da ake amfani da su wajen aikata miyagun laifuka.

KU KUMA KARANTA: Mun gano haramtattun hanyoyin da ake satar man fetur a Najeriya – NNPC

Sun samu wannan nasara ce sakamakon aiki da bayanan sirri da suka samu game da irin haramtattun ayyukan dake gudana ne a kewayen yankin Buguma dake karamar hukumar Asari-Toru.

Sannan sojojin suka gudanar da gagarumin samame, lamarin da ya kai ga gano wani makeken tafki da kuma kwale-kwalen katako mai dauke da litar man sata sama da dubu 37,000.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A yankin Ogajiama na yankin Buguma/Bakana, da ke karamar hukumar Asari-Toru, sojoji sun yi artabu da masu tada zaune tsaye wato ƴan bindiga wadanda suka tsere bisa amon wutar da suka ji.

Leave a Reply