‘Yan Syria masu gudun hijira a Turkiyya sun fara komawa ƙasarsu

0
21
'Yan Syria masu gudun hijira a Turkiyya sun fara komawa ƙasarsu

‘Yan Syria masu gudun hijira a Turkiyya sun fara komawa ƙasarsu

Aƙalla ‘yan Syria miliyan 3 ne suke neman mafaka a Turkiyya bayan da suka tsere daga ƙasar ta Syrai bayan da yaƙi ya ɓarke a 2011.

A jiya Jumma’a, ministan cikin gidan Turkiyya ya ce kimanin ‘yan Syria dubu 31,000 masu gudun hijira a Turkiyya da wasu kasashe ne ne suka koma kasar su bayan da aka hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad a farkon watan nan.

Akalla ‘yan Syria miliyan 3 ne suke neman mafaka a Turkiyya bayan da suka tsere daga kasar ta Syrai bayan da yaki ya barke a 2011.

Kifar da gwamnatin Assad da akayi a baya bayan nan ya baiwa ‘yan kasar ta Syria masu gudun hijira a Turkiyya da wasu kasashe kwarin gwiwar komawa kasar su.

Komawar ‘yan Syria masu gudun hijira kasar su ya biyo bayan alkawarin da kasar Turkiyya ta yi cewa zata tallafawa kasar dasamar da wutar lantarki a Syria, sannan zata taimaka mata ta gyara na’urorin makamashin ta, abinda aka ambato ministan ya fada kenan a ranar Jumma’a.

Leave a Reply