Ƙasar Masar za ta aika da dakarunta aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia

0
14
Ƙasar Masar za ta aika da dakarunta aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia

Ƙasar Masar za ta aika da dakarunta aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia

Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty ya ce kasar za ta shiga cikin sabon aikin wanzar da zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afrika a Somaliya.

“Masar za ta shiga aikin ne bayan Somaliya da Kwamitin Tsaro na Kungiyar AU sun bukaci ta yi hakan,” in ji Badr Abdelatty yayin da yake wata zantawa da takwaransa na Somaliya Ahmed Moalim Fiqi lokacin da suke ganawa da manema labarai ranar Litinin.

An fara samun zaman tankiya a yankin Kusurwar Afrika bayan da Ethiopia ta kulla yarjejeniya a watan Janairu da yankin Somaliland wanda ya balle daga Somaliya kuma hakan ya sa kasar ta kara karkata bangaren Masar wacce ba ta ga-maciji da Ethiopia.

Kalaman Abdelatty yana zuwa ne kafin cikar wa’adin aikin musamman na wanzar da zaman lafiya na Kungiyar AU (ATMIS) a ranar 31 ga watan Disamba, inda daga bisani za a fara aiki da wani sabon aikin wanzar da zaman lafiya mai taken (AUSSOM).

KU KUMA KARANTA: Birtaniya ta tura wa Ukraine ƙunshin makamai mafi girma don yaƙar Rasha

A ranar Litinin Abdelatty ya jaddada cewa “Somaliya za ta kasance kasa mai cikakken ’yancin cin gashin kanta” kuma ya ce za a yi watsi da duk “wani yunkuri da raba kan kasar ko kawo tsagaro kan cikakken ’yancinta da kuma zaman lafiyarta.”

A wannan wata Turkiyya ta kulla yarjejeniya da niyyar kawo karshen rashin jituwar da ke tsakanin Somaliya da Ethiopia.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana sulhun da aka samu da wani abu “mai cike da tarihi” kuma Kungiyar AU da Amurka da Tarayyar Turai (EU) sun yi maraba da sulhun da aka cim ma.

Tun da farko Somaliya ta bukaci cire dakarun Ethiopia daga aikin wanzar da zaman lafiyar AU, kuma kasar ta yi maraba da shigar Masar cikin tawagar.

Ministan harkokin wajen Masar bai yi karin haske ba kan yadda kasar za ta tura tawagarta, sai dai ya ce duka kasashen biyu suna aiki tare don samar da alaka mai muhimmanci ga kowannensu..
A watan Agusta, Masar ta kulla wata yarjejeniyar soji da Somaliya yayin wata ziyara a da Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud a birnin Cairo.

A watan Oktoba yayin wani babban taro a babban birnin Eritrea wato Asmara, Masar da Eritrea da kuma Somaliya sun kulla wani sabon kawance ba tare da sanya Ethiopia a ciki ba.

Masar ta dade ba ta jituwa da Ethiopia kan batun ginin wani sabon babbar madatsar ruwa a Kogin Nilu wadda take barazana ga ruwan da Masar ɗin take samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here