No menu items!

Sample Page Title

Date:

Jami’an tsaro sun tarwatsa sansanin Lakurawa a Sokoto da Kebbi

Dakarun rundunar Sojoji ta musamman da babban hafsan Sojin ƙasa, Janar Christopher Musa ya tura, ta yi nasarar fatattakar ‘yan ƙungiyar Lakurawa da dama da ke a jahohin Sokoto da Kebbi.

Kwamandan atisayen Fansan Yamma, Manjo Janar Oluyinka Soyele, ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ƙara da cewa, rundunar ta lalata sansanoni 22 na ‘yan ta’addan a jihohin.

Ya ce sun yi nasarar ƙwato bindigu hudu, ƙirar PKT 409 7.62mm NATO da harsashi na musamman 94 masu tsahon 7.62mm a yayin fafatawa da ‘yan ƙungiyar ta Lakurawa.

Ya ƙara da cewa an samu nasarorin ne ta hanyar sabbin salon hare-hare da suke kai wa ‘yan bindigar na Lakurawa wanda ya kai ga lalata sansanoninsu.

KU KUMA KARANTA: Jamian tsaro a Benuwe sun lalata maɓoyar ’yan bindiga

Soyele ya ci gaba da bayyana cewa an zaɓo dakarun ne tare basu horo na musamman don aikin fatattakar ‘yan ta’addan Lakurawan, inda ya umarce dakarun sojin da su bi ƙa’idojin aiki tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma yayin bayar da tsoro da ma sauran ayyukansu na yau da kullum.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...