Kotun ɗaukaka ƙara ta mayar da Muhuyi Magaji kan muƙaminsa

0
42
Kotun ɗaukaka ƙara ta mayar da Muhuyi Magaji kan muƙaminsa

Kotun ɗaukaka ƙara ta mayar da Muhuyi Magaji kan muƙaminsa

Kotun ɗaukaka ƙara ta Abuja ta rushe dakatarwar da aka yiwa shugaban hukumar yaƙi da almundahana ta Kano, Muhuyi Magaji daga kan muƙaminsa.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da kotun mai Alƙalai 3, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Umaru Fadawu ta zartar, wanda ya bayyana dakatarwar da lamarin mai cutarwa kuma tauye hakkin Muhuyi Magaji ne na jin ba’asinsa.

KU KUMA KARANTA:Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga sallamar ma’aikata 1000

Da yake yanke hukuncin a yau Juma’a, Mai Shari’a Fadawu ya bayyana cewa, “dakatarwar da kotun da’ar ma’aikata ta yi muhuyi ba ta dace ba kuma ta sabawa tsarin jin ba’asin ko wane bangare. Kuma mun umarci a mika batun ga wani rukunin alkalan kotun da’ar ma’aikata na daban.”

A ranar 4 ga watan Afrilun 2023 aka dakatar da muhuyi magaji, sakamakon zarge-zargen aikata ba dai dai ba da kotun da’ar ma’aikatan ke yi masa.

Kotun da’ar ma’aikata, karkashin jagorancin Mai Shari’a Danladi Umar, ta umarci Gwamnan Kano, Abba Yusuf, da sakataren gwamnatin jihar su nada wanda zai jagoranci hukumar yaki da cin hancin a mataki na riko har sai an kammala sauraron karar.

Leave a Reply