Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga sallamar ma’aikata 1000

0
52
Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga yiwa ma’aikata 1000 ritaya

Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga sallamar ma’aikata 1000

Majalisar wakilai ta ɗauki wani mataki da wasu ke gani abin alheri ne bayan jin irin koke koken da suka riƙa tashi kan batun korar ma’aikata 1,000 da Babban Bankin Najeriya ya ce zai yi, yayinda kwararru a fanin tattalin arziki ke gani akwai.

 Majalisar Wakilai ta ba Babban Bankin Najeriya umurnin dakatarda sallaman ma’aikatan bankin 1,000 ɗaya da ya yi niyya yi, domin ta Kafa Kwamiti na Musamman da zai yi bincike kan yadda za a yi wa ma’aikata 1,000 daya ritaya a lokaci daya kuma har za a biya su kuɗin sallama da ya kai Naira Biliyan 50 a wannan lokaci da kasar ke fama da rashin kuɗi.

KU KUMA KARANTA: Yadda Emefiele ya mallaki bankuna 3 ta ɓarauniyar hanya

Majalisar ta ce kwamiti ya yi bincike kan ƙai’doji da tsari da halarcin aikin.

A hirar shi da Muryar Amurka, ɗan Majalisa mai wakiltan Yamaltu Deba ta Jihar Gombe Inuwa Garba ya yi karin haske cewa, Majalisa ita ce mai sa ido a yadda ake gudanar da mulki a ƙasa, saboda haka tana da hurumin ɗaukan matakai kamar yadda doka ta tanada.

Inuwa ya ce babu yadda za a yi Majalisa ta bari irin waɗannan matakai suna faruwa ba tare da ta duba yiwuwar haka a bisa tsari ba, dalili ke nan inji shi, Majalisa ta kafa Kwamitin.

Shi kuwa masanin tattalin arziki na ƙasa da ƙasa, Yusha’u Aliyu ya yi tsokaci ne kan abinda CBN ya yi inda ya ce ba daidai ba ne a wayi gari a cikin wannan yanayi da ƙasa ke ciki, a yi wa mutane 1,000 ɗaya ritaya haka kawai.

Yusha’u ya ce ya kamata a bi tsarin aiki,da yawan shekaru da mutanen suka yi kafin a dauki matakin sallamar su, saboda a yi masu adalci wajen biyan su kudaden su yadda ya kamata..

A nashi bayanin, mai nazari kan al’amuran yau da kullum Abubakar Aliyu Umar, ya ce yanzu ne ya ke ganin ƙoƙarin ‘yan Majalisa kan kokarin sauraren kokekoken al’umma. Abubakar ya ce wannan yunkuri na dakatar da sallaman wadannan ma’aikata sai an yi bincike, abu ne mai kyau, ga kuma batun dakatar da sauya fasalin harajin kasa da suka yi, duka waɗannan abubuwa ne na yabo.

Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne domin bin kaidojin aikin gwamnati da kuma dokokin Ƙwadago.

Leave a Reply