Adefunke Adeyemi ya zama shugaban AFCAC a karo na biyu

0
31
Adefunke Adeyemi ya zama shugaban AFCAC a karo na biyu

Adefunke Adeyemi ya zama shugaban AFCAC a karo na biyu

An sake zaɓen Adefunke Adeyemi a matsayin babbar sakatariya a hukumar kula da sufurin jiragen saman Afirka (AFCAC) a yayin karo na 35 na babban taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a birnin Brazzaville, na ƙasar Congo.

Mashawarci na musamman a kan harkokin yada labarai ga ministan sufurin jiragen sama, Tunde Moshood, ne ya bayyana hakan a sanarwar daya fitar a yau Alhamis.

A cewarsa, ministan sufurin jiragen da bunkasa zirga-zirgar sararirin samaniya, Festus Keyamo, ya halarci taron da ke gudana a kasar Congo Brazzaville kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen sake zabarta.

KU KUMA KARANTA:Shugaba Tinubu na zawarcin masu zuba jari daga ƙasar Faransa

Moshood ya kara da cewa ministan ya jagoranci muhimmiyar tattaunawar diflomasiya da mambobin kungiyar hada kan Afrika ta AU, inda ya nemawa takarar Adeyemi goyon baya.

“Wannan nasara ba ta takaita ga Najeriya ba kawai illa nasara ce ga ilahirin harkar sufurin jiragen saman nahiyar Afirka,” a cewar keyamo jim kadan bayan zaben.

Leave a Reply