No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ƙasar Isra’ila ta kai hari wani sansanin soji, ta jikkata mutum 18

Isra’ila ta kashe sojan Lebanon da jikkata mutum 18 a wani hari ta sama da ta kai wani sansanin sojin Lebanon, kamar yadda sojojin suka sanar a ranar Lahadi.

Wata sanarwa da sojojin suka fitar ta bayyana cewa harin ya faɗa kan cibiyar soji da ke al-Amiriya da ke kan titin Al-Qalila-Tyre.

Sanarwar ta ƙara da cewa harin ya yi matuƙar ɓarna ga sansanin sojin.

KU KUMA KARANTA: Israila ta kashe Falasɗinawa 7 tare da raunata wasu da dama

Isra’ila ta fara yaƙi da kasar Lebanon, inda ta kaddamar da wani farmaki ta sama a karshen watan na Satumba, kan abin da ta ce tana kai wa kungiyar Hezbollah hari.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...