Gwamnatin Bauchi ta amince da ₦70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

0
20
Gwamnatin Bauchi ta amince da ₦70,000  a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnatin Bauchi ta amince da ₦70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya sanar da cewa, gwamnatinsa za ta fara biyan sabon tsarin albashi na ƙasa daga watan Nuwamban 2024.

Sabon tsarin wanda ya kasance Naira 70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ne gwamnatin ya amince da shi.

Bala Muhammad ya sanar da hakan ne a yayin da ke buɗe taron majalisar zartarwa na jihar (SEC), inda ya ce, zaman nasu ya ƙunshi tattauna batutuwan gabatar da kasafin kuɗin 2025 ga majalisar dokokin Jihar.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta amince da biyan ₦71,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi 

Gwamnan ya yi bayanin cewa tunin aka yi dukkanin tsare-tsaren da suka dace na biyan sabon tsarin albashi a cikin kasafin kuɗi na 2025, wanda a tsarin ma’aikatan jihar za su fara cin gajiyar sabon albashin daga watan Nuwamba.

Gwamnan ya ce, jihar za ta tashi tsaye wajen taimaka ma manoma domin ƙara himma wajen samar da abinci mai inganci da kyautata tattalin arziki a faɗin jihar.

Gwamna Bala ya nuna damuwa kan rahoton hukumar fitar da alƙaluma da ya bayyana jihar Bauchi cikin ɗaya daga jihohi masu fama da matsanancin talauci.

Ya ce rahoton ya zaburar da gwamnatin sa tare da kira ga majalisar da ta laluɓo hanyoyin samar da ayyukan jin ƙai, kana ya jaddada aniyar gwamnati na biyan basukan giratuti da tsoffin ma’aikata ke bi don ɗaukar mataki akansu cikin gaggawa.

Leave a Reply