Jami’an tsaro sun kama ‘yan bindiga 3 da mai yin safarar makamai

0
74
Jami'an tsaro sun kama 'yan bindiga 3 da mai yin safarar makamai

Jami’an tsaro sun kama ‘yan bindiga 3 da mai yin safarar makamai

Dakarun rundunar sojin Operation Whirl Stroke sun kama wasu mutane uku da suke zargin ‘yan bindiga ne tare da wani mai safarar makamai da ke da alaka da ‘yan ta’adda a Jihar Taraba.

An samu nasarar ne sakamakon samun sahihan bayanan sirri, inda aka ƙaddamar da wani samame na musamman a ranar 7 ga watan Oktoba a yankin Andemin da ke karamar hukumar Karim Lamido.

Bayanan sun kuma taimaka wajen kama wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a kauyen jeb-jeb, da ke kan iyakar jihohin Taraba da Filato.

KU KUMA KARANTA: Yan bindiga satar makaman jami;an tsaro suka yi – Ministan Tsaro

Hakan na ƙunshe n a cikin wata sanarwar da daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Kyaftin Olubodunde Oni, ya raba wa manema labarai.

Ya bayyana cewar ‘yan bindigar da aka bayyana sunayensu da Adamu Abubakar da Muhammad Bello da Musa Adamu na da hannu a jerin laifukan da aka aikata a yankin.

Daga cikin laifukan har da fashi da makami da satar mutane da kai wa ƙauyuka munanan hare-hare.

Leave a Reply