Mu bai wa matatar Ɗangote goyon baya domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa – Shugaban IPMAN

0
25
Mu bai wa matatar Ɗangote goyon baya domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa - Shugaban IPMAN

Mu bai wa matatar Ɗangote goyon baya domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa – Shugaban IPMAN

Ƙungiyar Dilallan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN), ta cimma yarjejeniya da Matatar Ɗangote kan fara dakon man fetur kai-tsaye daga wajen su.

Yarjejeniyar ta samu ne bayan makonni da aka ɗauka ana tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu kan samar da man fetur a sauƙaƙe kuma a farashi mai rahusa.

Da yake magana da manema labarai a Abuja, Shugaban IPMAN, Abubakar Garima, ya ce yarjejeniyar za ta inganta haɗin gwiwa tsakaninsu, wanda zai taimaka wajen samar da isasshen man fetur mai rahusa a faɗin ƙasar.

Garima, ya yi ƙira ga mambobin IPMAN da su bai wa matatar Ɗangote goyon baya domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.

“Bayan ganawa da Aliko Ɗangote da mahukuntansa a Legas, muna farin cikin sanar da cewa Matatar Ɗangote za ta samar wa IPMAN da man fetur, dizal, da kalanzir kai-tsaye don rabawa zuwa manyan rumbunan ajiyarmu da wuraren sayarwa,” in ji shi.

Ya kuma shawarci mambobin IPMAN da su dogara da Matatar Ɗangote da matatun man Najeriya, wanda zai ƙara samar da ayyukan yi da kuma tallafa wa manufofin cigaba na Shugaba Bola Tinubu.

Tun da farko a watan Nuwamba, IPMAN ta bayyana cewa tsadar jigilar mai daga Matatar Ɗangote ta sa wasu dilallai neman mai rahusa.

KU KUMA KARANTA: NNPCL ta musanta zargin MURIC na yi wa matatar man Ɗangote maƙarƙashiya.

Rashin cimma yarjejeniya tsakanin IPMAN da Ɗangote ya janyo tsaiko da ƙalubale wajen samar da man fetur a baya.

Leave a Reply