An dawo da wutar lantarki a wasu yankunan arewacin Najeriya – TCN

0
70
An dawo da wutar lantarki a wasu yankunan arewacin Najeriya - TCN

An dawo da wutar lantarki a wasu yankunan arewacin Najeriya – TCN

Kamfanin TCN mai raba wutar lantarki a Najeriya ya ce an gyara layin wutar Ugwuaji-Apir mai karfin 330kV da yammacin Laraba bayan da injiniyoyi suka kammala ayyukansu.

Wata sanarwa da kamfanin ya fitar ɗauke da sa hannun kakakinsa Ndidi Mbah, ta ce yanzu “lafia, Makurdi, Jos, Kaduna, Kano, Bauchi da Gombe na da wuta.”

An doshi kusan makonni biyu babu wutar lantarki a ɗaukacin arewacin Najeriya sanadiyyar barnata kayayyakin wutar lantarki da ‘yan fashin daji suka yi akan layin na Ugwuaja-Apir.

KU KUMA KARANTA: Shugaban ƙasa ya nuna damuwarsa kan rashin wuta a arewacin Najeriya

“Yayin da ake ci gaba da gyare-gyaren, tawagar injiniyoyinmu na shirin fara aiki akan layin 330Kv na biyu.” In ji Mbah.

Rahotanni sun nuna cewa katsewar wutar lantarki ta haifar da ɗumbin asara ga masana’antu, ‘yan kasuwa da kananan ma’aikatu cikin kwanakin da aka kwashe babu wutar.

Ƙungiyar Masana’antu ta Najeriya a Kano ta ce mambobinta sun tafka asarar biliyoyin naira cikin takin lokacin da aka kwashe babu lantarki a sassan arewacin Najeriyar.

Leave a Reply