Gwamnatin Kano ta amince da biyan ₦71,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi 

0
41
Gwamnatin Kano ta amince da biyan ₦71,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi 

Gwamnatin Kano ta amince da biyan ₦71,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnatin Jihar Kano ta amince za ta biya N71,000 a matsayin albashi mafi karanci ga ma’aikatan jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin karɓar rahoton kwamitin tattaunawar ayyukan gwamnati ƙarƙashin jagorancin shugaban ma’aikatan jihar a ofishinsa a ranar Talata.

Ya ƙara da cewa sabon albashin zai fara aiki daga watan Nuwamba 2024.

Sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ambaci Gwamna Yusuf yana cewa, jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin da ke da dumbin ma’aikatan gwamnati.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kebbi za ta fara biyan ₦75,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

“Ina so in jaddada cewa Jihar Kano na da ɗaya daga cikin jihohin masu mafi yawan ma’aikata a Najeriya, duba da irin yawan al’umarmu da bukatunmu na cikin gida da kuma matsi ta fannin kuɗaɗen shiga na gida da muka gada, mun yanke shawarar aiwatar sabon albashi na ƙasa akan N71,000.” Yusuf ya ce.

Gwamna Yusuf ya ce aiwatar da mafi ƙarancin albashi zai ƙara wa jihar nauyin biyan albashi na wata-wata da sama da Naira biliyan 6, yana mai cewa za a nemi ƙarin Naira biliyan 7 don buƙatun ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Leave a Reply