Wasu ‘yan bindiga sun hallaka fararen hula 8

0
55
Wasu 'yan bindiga sun hallaka fararen hula 8

Wasu ‘yan bindiga sun hallaka fararen hula 8

Aƙalla mutane 8 sun mutu a arewacin Togo a wani saban harin da ‘yan bindiga suka kai a arewacin ƙasar.

Majiyoyi daga wasu mazauna ƙauyukan sun shaida cewa  ‘yan bindigar sun zo ne a cikin daren juma’a wayewa safiyar asabar inda bayan sunyi kutse a wani gida  da aka tsugunar da ‘yan gudun hijira  suka yi wa mai gidan da sauran mutane 7 kisan gilla.

Majiya ta ƙara da cewa a wanan karon  ‘yan bindigar sun hari ƙauyen Malgabangou  ne an kuma kiyasta aƙalla mutane 8 sun mutu.

Wanan shi ne karo na biyu a cikin makwani biyu da yankin ya fuskanci harin ‘yan bindiga.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Zamfara sun harbi babban kwamandan dakarun sa kai

Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, sai dai a baya ƙungiyar mayaƙa masu iƙirarin Jihadi ta JNIM ta sha kai hare hare a baya a wanan yankin.

Tun daga shekara 2021, ƙauyukan dake yammacin gunduma Kpendjal a ƙasar ta Togo ke fuskanta hare haren ‘yan bindiga masu ɗauke da makamai.

Leave a Reply