An gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Kano

0
30
An gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Kano

An gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Kano

Zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi a jihar Kano a ranar Asabar, 26 ga watan Oktoba na 2024, ya gamu da ƙalubalen rashin fitowar Jama’a domin kaɗa ƙuri’a kuma Jami’an tsaro musamman ‘yan sanda su ma ba su fito aikin ba da tsaro ba.

Zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi a ranar Asabar 26 ga watan Oktoba na 2024 a jihar Kano ya fuskanci ƙarancin fitowar Jama’a su kaɗa ƙuri’a sannan, Jami’an tsaro musamman ‘yansanda ba su fito don tabbatar da tsaro ba.

A galibin mazabu da rumfunan zaben da wakilin mu Mahmud Kwari ya kewaye a sassan jihar ta Kano, duk ya tadda karancin mutane sosai, yayin da wasu a wuraren kuma, babu labarin kai kayayyakin zaben ma, kuma kalilan daga cibiyoyin da suka samu kayayyakin zaben an kammala zaben da karfe goma zuwa sha daya na rana.

Suma Jami’an tsaro, musamman ma ‘yan sanda sun kauracewa wuraren kada kuri’a don bada tsaro, kuma ta yuwu hakan ya kasance ne saboda hukuncin babbar kotun tarayya ta Kano na haramta musu halartar cibiyoyin zaben.

KU KUMA KARANTA:An samu ƙarancin fitowar jama’a, a zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Wasu daga cikin mutanen da suka je rumfunan zabe domin kada kuri’ar su sun ce sunyi amfani da dokar da kasa ta basu na jefawa wanda suke so kuri’a ne, kuma ‘yan kwamitin tsaro da suka kunshi Jami’an Vijilanti da na Karota sun bada kariyar tsaro a rumfunan zabe.

Baya ga dambarwar shari’ar da ta dabaibaye sha’anin zaben da yanke kauna da adalci ko sahihanci akan harkar zaben kananan hukumomi a Najeriya, matsin rayuwa da ake fama da shi a kasar na daga cikin manyan dalilan da suka hana mutane a jihar Kano kauracewa wannan zabe na 26 ga wannan wata na Oktoba.

Manyan Jam’iyyun hamayya na PDP da APC ba su shiga zaben ba, amma a cewar Farfesa Sani Lawan Malumfashi shugaban hukumar zaben ta Kano 6 daga cikin kananan Jam’iyyu a Najeriya da suka haɗa AA, AAC ACCORD, ADC APM da kuma Jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano sun shiga zaben.

Leave a Reply