Tinubu ya na aiki sosai, amma waɗanda ya naɗa a muƙamai ba sa yayata wa — APC

0
42
Tinubu ya na aiki sosai, amma waɗanda ya naɗa a muƙamai ba sa yayata wa — APC

Tinubu ya na aiki sosai, amma waɗanda ya naɗa a muƙamai ba sa yayata wa — APC

Tony Okocha, shugaban riƙo na jam’iyyar APC a jihar Rivers, a jiya Lahadi a Abuja, ya bayyana cewa ba a yayata nasarorin da Shugaba Bola Tinubu ya samu a mulkin sa a halin yanzu.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke magana a wani taro da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, inda ya kara da cewa akwai bukatar ministocin Tinubu su kara kaimi wajen fadakar da ‘yan Najeriya irin nasarorin da gwamnatin sa ta samu.

“Ba a yayata irin nasarorin da shugaba Tinubu ya samu domin yawancin ministocinsa sun kasa yin abin da ake bukata kuma ba sa kara wa gwamnatin kima a idon ƴan ƙasa.

KU KUMA KARANTA:Tinubu ya umarci ministoci, shugabannin soji su rage adadin motocin da suke yawo da su

“An wuce lokacin da za a ce kada a ka riƙa kurara kan ka. A kwanakin nan dole ne ku busa kahon ka da ƙarfi,” in ji shi.

Ya kara da cewa duk da kalubalen da ake fuskanta gwamnatin Tinubu ba ta yi abun a yaba duba da yadda ta gaji mummunan yanayi daga gwamnatin da ta gabata.

Leave a Reply