Tinubu ya umarci ministoci, shugabannin soji su rage adadin motocin da suke yawo da su

0
58
Tinubu ya umarci ministoci, shugabannin soji su rage adadin motocin da suke yawo da su

Tinubu ya umarci ministoci, shugabannin soji su rage adadin motocin da suke yawo da su

Ɗaukar wannan mataki a cewar Fadar Shugaban ƙasar, yunƙuri ne na rage kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa.

Shugaba Bola Tinubu ya taƙaita adadin motocin da ke ayarin Ministoci, da ƙananan Ministocin, da Shugabannin Hukumomin Gwamnatin Tarayya zuwa motoci uku kacal a tawagarsu ta aiki.

Fadar gwamnatin ƙasar ta bayyana wannan matakin rage kashe kuɗi a ranar Alhamis a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinsa Bayo Onanuga.

KU KUMA KARANTA:Shugaba Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta tabbatar da sabbin ministoci

A watan Janairun wannan shekara, Shugaba Tinubu ya dauki muhimman matakai don rage kashe kudaden gwamnati, ta hanyar rage adadin mutanen da ke rakiyarsa a tafiyarsa zuwa kasashen waje daga mutum 50 zuwa mutum 20. A tafiye-tafiyen cikin gida, ya rage zuwa mutum 25.

Kazalika, ya rage tawagar Mataimakin Shugaban kasa zuwa mutum biyar a tafiye-tafiyen kasashen waje da kuma mutum 15 don tafiye-tafiyen cikin gida.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci Mai Ba da Shawara kan Tsaron Kasa da ya tuntubi Sojoji, Hukumomin Tsaro, da sauran hukumomin tsaro na fairn kaya don tsara adadin da ya dace na motocin da za su rika bin ayarinsu.

Leave a Reply