Ministan tsaron Najeriya ya ba da umarnin a kamo masa Bello Turji a duk inda yake

0
50
Ministan tsaron Najeriya ya ba da umarnin a kamo masa Bello Turji a duk inda yake

Ministan tsaron Najeriya ya ba da umarnin a kamo masa Bello Turji a duk inda yake

Ministan tsaron Najeriya, Muhammed Badaru Abubakar, ya umarci dakarun Najeriya ƙarƙashin “Operation Fansar Yamma” da su kamo shugaban ‘yan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, Bello Turji.

Umarnin na Badaru na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da Shugaba Bola Tinubu ya yi garambawul ga majalisar ministocinsa.

KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga satar makaman jami’an tsaro suka yi – Ministan Tsaro

Kalaman Badaru sun zo ne makonni uku bayan Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa kwanakin Turji sun kusa karewa.

Yayin da yake jawabi ga sojoji a hedikwatar Runduna ta Daya da ke Gusau, Jihar Zamfara, a ranar Alhamis, Badaru ya kara wa sojoji kwarin gwiwa, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu yana bibiyar ayyukansu a watannin da suka gabata kuma ya ga ci gaba mai kyau.

“Ina da tabbaci daga kwamandan sojoji kuma na ji dadi, na tabbata za mu cimma burinmu. Kuna shirye ku gama da su? Kuna shirye ku kawo karshensu? Don Allah ku kawo min Turji.” Badaru ya ce kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Badaru ya kai ziyarar ta Gusau ne da nufin samun bayanan kan yadda ake tafiyar da ayyukan soji a yankin da ‘yan bindiga suka addaba.

Leave a Reply