Gwamnatin Kebbi za ta fara biyan ₦75,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

0
125
Gwamnatin Kebbi za ta fara biyan ₦75,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnatin Kebbi za ta fara biyan ₦75,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnatin jihar Kebbi, ta amince da biyan Naira dubu saba’in da biyar a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan jihar.

Da yake jawabi jim kadan bayan sanya hannu kan dokar, Gwamna Nasir Idris, ya bayyana cewa bayan karɓar rahoton kwamitin haɗin gwiwa na ƙungiyar ƙwadago da gwamnati tare da shawarwari guda uku, gwamnatin ta amince da zabi na biyu na Naira dubu 75 a matsayin sabon mafi karancin albashi.

Gwamnan, ya ce za a bada mafi ƙarancin albashin ne a dukkan ɓangarorin  ma’aikatan gwamnati da na ƙananan hukumomi.

Ya umarci ma’aikatar kuɗi ta jihar da ta fara biyan sabon mafi karancin albashin nan da kwanaki uku.

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC, Kwamared Joe Ajaero da majalisar zartarwarsa sun halarci wajen rattaba hannu kan mafi ƙarancin albashin ma’aikatan a dakin taro na gidan gwamnati dake Birnin Kebbi.

Leave a Reply