Tinubu ya rushe ma’aikatar ci gaban yankin Neja-Delta da ta wasanni

0
112
Tinubu ya rushe ma'aikatar ci gaban yankin Neja-Delta da ta wasanni

Tinubu ya rushe ma’aikatar ci gaban yankin Neja-Delta da ta wasanni

Daga Ibraheem El-Tafseer

A cikin babban gyara ga tsarin gwamnatin tarayya, Shugaba Bola Tinubu da Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a yau Laraba sun amince da manyan sauye-sauye, ciki har da rushe Ma’aikatar Yankin Neja-Delta da Ma’aikatar Raya Wasanni.

Waɗannan ma’aikatun za a maye gurbinsu da sabbin hukumomi don inganta aiki da sauƙaƙe tafiyar da gwamnati.

Bayo Onanuga, mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin yada labarai ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

“A fannin wasanni, Hukumar Wasanni ta Ƙasa za ta ɗauki nauyin ayyukan da Ma’aikatar Wasanni ke yi, wanda ke nuna sabon tsarin gudanar da cigaban wasanni a faɗin ƙasa.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya rushe shugabannin ƙananan hukumomin jihar 44

“Wannan sabon tsari yana nufin ƙarfafa ikon hukumar da kuma haɓaka damar ta wajen tallafawa wasanni a kowane mataki”

“Bugu da ƙari, FEC ta amince da haɗe Ma’aikatar yawon buɗe ido da Ma’aikatar Al’adu da Tattalin Arzikin Kirkira. An tsara wannan haɗakar ne domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin yawon buɗe ido, al’adu, da sashin kirkirar da ake ganin suna da mahimmanci wajen faɗaɗa tattalin arzikin ƙasa da haɓaka ci gaba.

An yanke waɗannan shawarar ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka yi a yau a Abuja, a wani ɓangare na ajandar Shugaba Tinubu na gyara tsarin gwamnatin tarayya da inganta ingancin gudanar da harkokin gwamnati.”

Leave a Reply