No menu items!

Sample Page Title

Date:

Tsadar Rayuwa: Wani mutum ya kashe kansa

Daga Idris Umar, Zariya

Wani mutum ya kashe kansa saboda tsadar rayuwa a maraban garin Kaba dake Lokoja jihar Kogi.

Wata mata da ta nemi a sakaya sunanta ta baiyana yadda lamarin ya faru ga jaridar Neptune Hausa ta wayar salula cewa, mamacin ya daɓawa kansa wuƙane a wuya da cikinsa yayin da ya sami wuƙa a wajan wani mai sayar da lemun zaƙi.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na yammacin jiya litinin 21/10/24 amma kafin ya rasu ya baiyana dalilinsa na yin haka.

Mamacin ya baiyana cewa, shi daga garin Tudun Wadan Ɗan Kade na jihar Kano yake kuma yana da mata da yara 3 a garin nasu amma bai faɗi sunansa ba.

KU KUMA KARANTA: Ƴan sanda a jihar Yobe sun kama wata mata da kashe mijinta da wuƙa

Mamacin ya ƙara da cewa wahalar rayuwace ta fito dashi domin bashi da wata hanyar da zai rinka ciyar da iyalinsa, yabi duk wata hanyar da zai tsara da rayuwarsa amma lamarin ya faskara bisa haka ya zaɓi ya bar duniya kawai.

Ƙarshe mamacin yace, a sanar da matarsa da yaransa su yafe masa don shi ya tafi kenan bazai dawoba.

Ya gama faɗin haka kenan sai rai yayi halinsa inji majijiyar tamu.

Amma bincike ya tabbatar da cewa bayan rasuwar nasa ne al’ummar musulmi na wannan anguwa sukai mashi salla kamar yadda Shari’a ya tanada.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...