No menu items!

Sample Page Title

Date:

‘Yan bindiga satar makaman jami’an tsaro suka yi – Ministan Tsaro

‘Yan Najeriya na ci gaba da tattaunawa a kan kalaman mai-baiwa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara a kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, da ya ce wasu jami’an tsaron Najeriya suna sayarwa ‘yan-bindiga makamai.

Ministan tsaron Najeriya Alh. Badaru Abubakar ya ce, makaman da ake samu a hannun ‘yan-bindiga na jami’an tsaron Najeriya, sun sace su ne yayin da suke kai hari.

Ministan tsaron Alh. Muhammadu Badaru Abubakar wanda ya kai wa rundunonin sojan Najeriya a Kaduna ziyarar wuni biyu, ya ce ganin yadda sojojin Najeriya suke ta hallaka manyan ‘yan-bindiga a arewa maso yamma ne yasa ya kai wannan ziyarar don karfafa musu gwiwa, sannan ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tunibu ya ce ya jinjinawa sojojin a madadin sa bisa irin na mijin kokarin da su ke yi don magance matsalar tsaro a arewa maso yammacin Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Dakarun tsaro a Borno sun daƙile wani harin Boko Haram

La’akari da zargin da mai-baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribado ya yiwa jami’an tsaron, ya sabawa kalaman ministan tsaron Najeriya ya sa wasu ‘yan-Najeriya yin kira da ya kamata a gudanar da bincike.

A game da batun bukatar sulhu da ‘yan-bindiga kuma, Muhammadu Badaru Abubakar ya ce babu yaki da ‘yan-bindiga ne burin gwamnati yanzu ba batun sulhu ba.

Batun hare-haren ‘yan-bindiga dai na cikin manyan matsalolin tsaron da suka addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya, sai dai ana sa ran cewa za a kafa sabuwar cibiyar tsaro da gwamnati ta sanar don hada ayyukan jami’an tsaron yankin baki daya wanda zai iya taimakawa wajen magance matsalar cikin gaggawa.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...