Hukuncin kotu yana kawo cikas ga aikin VIO a wani ɓangaren – Masana

0
54
Hukuncin kotu yana kawo cikas ga aikin VIO a wani ɓangaren - Masana

Hukuncin kotu yana kawo cikas ga aikin VIO a wani ɓangaren – Masana

Masana da mahukunta sun ce Hukuncin da babbar kotu ta yanke na haramtawa hukumar VIO tsarewa ko kuma cin tarar direbobin motoci a birnin tarayya Abuja, ya kawo cikas ga harkokin su na samun kuɗaɗen shiga da kuma kaiwa ga ƙara yawan direbobin dake saɓa ƙa’idar tuƙi a Abuja.

Wasu mazauna babban birnin tarayyar Najeriya, suna ci gaba da nuna amincewar su da umarnin wata babbar kotu mai zama a tarayyar Najeriya Abuja, a ranar 2 ga watan Oktoba nan mai ci, inda ta yanke hukuncin da ya haramtawa ma’aikatar VIO tsarewa, kamawa, ko cin tarar direbobin motoci sakamakon irin korafe-korafen cin zarrafi da rashin bin ka’ida wajen aiwatar da aikinsu da ake zargin jami’an da aikatawa.

Wani mazaunin birnin na Abuja kuma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum, Abubakar Muhammad Jega, ya ce, har yanzu al’umma na marhaban da umarnin kotu a kan hana VIO tsarewa ko cin tarar direbobi ganin yadda suke haddasa hadurra a dalilin rashin bin ka’ida da rashin sanin makamar aikin nasu.

Wata kwararriya a fannin sadarwa dake zaune a birnin Abuja, ta ce ci gaba da bin umarnin kotun a bangare guda zai dakile ayyukan kin bin dokoki ga direbobi, a daya bangaren kuma ya kamata a duba dokokin aikin ma’aikatar ta VIO don kawo karshen zargin cin hanci da rashawa.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin tarayya ta ba da kwangilar fara gyaran titin Abuja zuwa Tafa

Wani jami’i a ma’aikatar na VIO da ya bukaci a sakaya sunan shi ya ce, lallai umarnin kotun ya kawo cikas ga hanyoyin samun kudadden shigar su, kuma a yanzu suna kan tuntuba da dukkan masu ruwa da tsaki a fannin bayan bin umarnin kotu a matsayin ma’aikatar dake karkashin gwamnatin Najeriya; nan ba da jimawa ba fannin dake kula da al’amurran doka na ma’aikatar gudanarwar a babban birnin tarayya Abuja zai sanar da matakin dauka nan gaba.

A wani bangare kuma, masani a fannin aiwatar da doka kuma daraktan tsaro na kungiyar a jinjinawa Najeriya, Kwamared Salihu Dantata Mahmud, ya cewa, umarnin mai Shari’a Maha bai dakatar da ayyukan VIO baki daya ba.

An dade ana kai ruwa rana a game da zargin take hakokkin direbobin motoci da ma’aikatar VIO da ma hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta Najeriya ke yi, lamarin da ya kai ga maka ma’aikatar kotu a lokuta da dama, wanda ya kai ga samun umarnin kotu na baya-bayan nan.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, an jimlar yawan hadurran motoci da aka samu a zangon farko na wannan shekara mai ci 2024 da ya kai dubu biyu da dari shida da sittin da biyu (2,662), wanda ke nuna samun raguwar haddura da kaso 2.0 daga zangon karshe na shekarar da ta gabata, 2023 inda alkaluman suka kai dubu biyu da dari bakwai da goma sha bakwai (2,717).

Leave a Reply