Ana nuna wa baƙaƙe bambanci launin fata da wariya a rayuwarsu ta yau da kullum – Harris

0
62
Ana nuna wa baƙaƙe bambanci launin fata da wariya a rayuwarsu ta yau da kullum - Harris

Ana nuna wa baƙaƙe bambanci launin fata da wariya a rayuwarsu ta yau da kullum – Harris

‘Yar takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar Democrat, Kamala Harris, ta yi gargaɗin cewa Donald Trump na jam’iyyar Republican zai nemi “ƙirƙirar dokar” da za ta haifar da koma baya ga baƙaƙen fata.

Ta kuma yi alƙawari a wata hira da mai gabatar da shirin rediyo, Charlamagne the God, cewa za ta yi ƙoƙarin samar da dokar da za ta magance yadda ake nuna banbanci wajen aiwatar da doka.

Trump ya zargi manufofin shige da fice na Harris da “lalata” al’ummomin baƙaƙen fata da al’umomin Latino yayin da yake gudanar da wani gangamin da daddare a Atlanta.

Harris ta ce ana nuna wa baƙaƙe bambanci launin fata da wariya a rayuwarsu ta yau da kullum – wajen mallakar gidaje, kiwon lafiya, ci gaban tattalin arziki har ma da zaɓe, tana mai cewa babu wanda ke da hujja da zai ki fita don kaɗa ƙuri’a.

KU KUMA KARANTA: Trump da Harris sun yi tir da zanga-zangar ƙin jinin Israila

Trump ya nace cewa bajin haure na shafar rayuwar baƙaƙen fata ta hanyar kwace musu ayyukan yi.

Ya kuma kwatanta shirin da Shugaba Biden da Mataimakiyarsa Kamala Harris suka samar akan iyakar Amurka a matsayin wani mataki na watsawa al’ummar baƙaƙen fata da na Latino ƙasa a ido.

Kalaman manyan ‘yan takarar biyu na zuwa ne yayin da Amurkawa ke shirin kaɗa ƙuri’a a ranar 5 ga watan Nuwamba.

Leave a Reply