Hauhawar farashin kayaki ta sake ta’azzara bayan lafawar watanni 2 – NBS

0
94
Hauhawar farashin kayaki ta sake ta'azzara bayan lafawar watanni 2 - NBS

Hauhawar farashin kayaki ta sake ta’azzara bayan lafawar watanni 2 – NBS

Bayan lafawar hauhawar farashin kayaki cikin watannin baya bisa alƙaluman hukumar ƙididdiga ta Najeriya, wasu sabbin alƙaluma da hukumar ta NBS ta fitar, sun nuna yadda farashin kayakin ya sake hauhawa a watan Satumban da ya gabata daga maki 32.15 zuwa maki 32.70.

Saɓanin yadda hauhawar farashin kayaki ya sassuto a watannin Yuli da Agusta, NBS ta ce matakin ƙarin farashin man fetur da mahukuntan Najeriyar suka yi a watan na Satumban ya sake ta’azzara matsalar ta tsadar kayaki.

Masana na kallon halin matsi da tsadar kayakin da al’ummar Najeriya ke fuskanta a yanzu haka ya iya zama mafi ƙololuwa da aka gani a wannan zamanin.

Cikin shekarar nan kaɗai mahukuntan Najeriyar sun ƙara farashin man fetur sau 5 a jare da juna, lamarin da ya sake ta’azzara matsalar ta hauhawar farashin kayaki musamman a ɓangaren da ya shafi kayan masarufi.

KU KUMA KARANTA: Farashin kayan abinci ya fara sauƙa a Najeriya

Tun gabanin sake hauhawar farashin dama ƙwararru sun yi hasashen cewa tsagaitawar hauhawar farashin ya iya zama na wucin gadi a Najeriyar lura da rashin matakan da za su sauƙaƙa rayuwa.

Bugu da ƙari manufofin kuɗin da ƙasar ke tafiya akai na ci gaba da takure marasa ƙarfi, a wani yanayi da babban bankin Najeriyar CBN ke shirin gabatar da sabon kuɗin ruwan da bankuna za su ci gaba da biya.

Leave a Reply