Za a fara amfani da sabuwar manhajar ilimi a watan Janairun 2025 – Ministan Ilimi 

0
50
Za a fara amfani da sabuwar manhajar ilimi a watan Janairun 2025 - Ministan Ilimi 

Za a fara amfani da sabuwar manhajar ilimi a watan Janairun 2025 – Ministan Ilimi

Ma’aikatar ilmin ta sanar da da cewar sabuwar manhajar ilimin firamare dana ƙaramar sakandare zasu fara aiki a faɗin Najeriya a watan Janairun 2025.

Ministan Ilmin, Farfesa Tahir Mamman, wanda ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki akan yadda za’a aiwatar da sabuwar manhajar a abuja, yace za’a fara amfani da sabuwar manhajar ilmin sakandare a watan satumbar 2025.

Farfesa Mamman ya bayyana cewar sabuwar manhajar zata warware matsalolin koyo da koyarwa dana samun aikin yi kasancewar sabon tsarin koyar da sana’o’in da aka kirkiro zai yi matukar tasiri wajen koyawa dalibai sana’o’in zamani.

KU KUMA KARANTA: Da ilimi ake samun kowace irin nasara a rayuwa – Dauda Lawal 

Ya ƙara da cewar za’a shafe watanni 3 masu zuwa ana sharar fage, ciki harda horas da malamai akan yadda zasu yi amfani da manhajar.

Leave a Reply