Isra’ila ba za ta samu galaba a kanmu ba – Sheikh Na’im Qassim

0
62
Isra'ila ba za ta samu galaba a kanmu ba - Sheikh Na'im Qassim

Isra’ila ba za ta samu galaba a kanmu ba – Sheikh Na’im Qassim

Daga Ibraheem El-Tafseer

Mataimakin sakatare janar na ƙungiyar Hezbollah, Sheikh Na’im Qassem ya gargaɗi Isra’ila cewa hanya ɗaya tilo da za a samu sulhu ita ce tsagaita wuta.

Sheikh Na’im ya ce “Hezbollah na da damar kare kanta ta hanyar kai hare-hare duk inda take son kaiwa” tun da dai Isra’ila ce ke kai wa Lebanon hare-hare.

Ya ƙara da cewa Isra’ilawa da ke arewacin Isra’ila za su ci gaba da fuskantar barazanar Hezbollah idan dai har Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a Lebanon da Gaza, inda ya ƙara da cewa “hanyar warware al’amarin ita ce tsagaita wuta… kuma ba za a iya samun galaba a kan Hezbollah ba saboda an shigo gonarmu ne”.

KU KUMA KARANTA: Mun shirya mayar da martani kan duk harin da aka kawo mana  Iran

Masana dai na alaƙanta jawabin Sheikh Na’im da yadda wasu ‘yan ƙasar Lebanon ke nuna tsoronsu ga yaƙin, inda ake tunanin an yi jawabin ne domin tausasa su, da kuma ƙara bayyana ƙarfin da Hezbollah ɗin take da shi.

Mataimakin sakatare janar ɗin ya kuma ja hankalin ‘yan ƙasar cewa idan har Isra’ila ta samu nasara a kan Hezbollah to lallai za ta sauya Lebanon ne da ma yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya.

Leave a Reply