‘Yan bindiga a Zamfara sun harbi babban kwamandan dakarun sa kai
A wata musayar wuta da aka yi a tasakanin ‘yan bindiga da dakarun tsaro na sakai CPG a jihar Zamfara, ‘yan ta’addar sun kashe mutane da dama inda suka raunata wasu ciki har da babban kwamandan rundunar ‘yan sa kan Janar Lawal B. Muhammad mai ritaya.
Rahotanni dai sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun tare hanyar Funtua zuwa Tsafe ne mai cike da cunkoson jama’a da yammacin ranar lahadi, inda suka far wa masu ababen hawa ciki har da Darakta janar na hukumar ta CPG.
Sannan a yayin wannan samamen ‘yan bindigar sun yi awun gaba da wasu fasinjoji da dama dake kan hanyarsu ta zuwa wurare daban-daban.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa wata majiya daga ma’aikatar tsaron cikin gida ta jihar Zamfara, wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ce shugaban na samun kulawa a wani asibiti da ke Gusau, babban birnin jihar.
KU KUMA KARANTA: Yansanda a Katsina sun kama wata mata kan rataye ɗan shekara 2
Wannan harin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da ‘yan bindiga suka kashe jami’an na CPG aƙalla takwas da wani direban motar sufuri a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar ta Zamfara.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi wa jami’an na CPG kwanton ɓauna ne kafin su an kara suka buɗe musu wuta.
Da yake bayani game da harin, babban kwamandan da aka harba ya bayyana cewa, bayan da ya fahimci cewa ‘yan bindigar na shirin kai hari a tsafe, sai ya tura jami’an CPG 105 zuwa ƙaramar hukumar tare da ajiye su a wannan wuri domin baiwa matafiya kariya ba tare da sanin sun musu riga Malam masallaci ba.
Sai gashi abin baƙin ciki ‘yan bindigar sukai musu kwanton ɓauna saboda sun kwana a wurin, a yayin da dakarun sa kan suke sauka sai suka bude musu wuta kuma suka kashe wasu daga cikinsu tare da jikkata wasu.