Wasu tubabbun ‘yan Boko Haram sun koma ruwa

0
123
Wasu tubabbun 'yan Boko Haram sun koma ruwa

Wasu tubabbun ‘yan Boko Haram sun koma ruwa

Rundunar sojin Najeriya ta nesanta kanta bayan sake bijirewa da wasu tubabbun mayaƙan Boko Haram suka yi inda suka sake komawa daji don ci gaba da ta’addanci.

Daraktan Sashen tattara bayanai kan irin arangamar da dakarun kasar ke yi a sassan kasar daban daban, Janaral Edward Buba wanda ke jawabi ga ‘yan jarida a hedkwatar tsaron kasar, ya ce ba sojoji ne ke da alhakin sake tsugunar da tubabbun mayakan ba.

Janaral Buba ya ce duk da haka abin bakin ciki ne a ce mutanen da a baya suka dau makami suke yakar kasarsu, bayan sun a je makami sun mika wuya, a ce sun kuma sake komawa daji.

Ya kara da cewa akwai bukatar dukkan masu ruwa da tsaki su hada karfi da karfe don tabbatar da sake duba tsarin ta yadda kwalliya za ta biya
kudin sabulu.

KU KUMA KARANTA:Dakarun tsaro a Borno sun daƙile wani harin Boko Haram

A dai wannan mako ne jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kimanin tubabbun mayakan sun sake gudu daji dauke da makaman da gwamnati ta
ba su suke taya sojoji yaki.

Bayan da suka mika wuya ne a cewar jaridar, gwamnatin jihar Borno ta horas da su ta hadasu aikin hadin gwiwa da sojoji da ke fafatawa da ‘yan Boko haram, a cikinsu ne kimanin guda goma sha shida suka sulale.

Gwamnatin jihar Borno dai nada wani shiri mai taken Borno Model – wato shirin afuwa na bayan yaki, na maida hankali ne akan raba tubabbun ‘yan ta’addan daga tsattsauran ra’ayi, gyaran tarbiyya, dawo dasu cikin jama’a don sake tsugunar da su, musamman ma wadanda ake jin suna da karancin hatsari.

Amma daya daga cikin tubabbun mayakan na Boko Haram ya ce abin da ya sa ‘yan uwan nasa suka sake tserewa shi ne tsananin kunci da suke ciki a hanun hukuma, sannan ba a cika masu galibin alkawurran da akai masu ba

Sai dai gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa tana sane sarai da yadda wasu tubabbun ‘yan ta’addan suka gudu, kuma tana hada gwiwa da jami’an tsaro don sake kamo su.

Wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai da harkokin tsaron cikin gida, Farfesa Usman Tat ya sanyawa hanu ya ce ‘yan ta’adda shida ne suka tsere ba goma sha uku ba kamar yadda ake ta yadawa,

Kwamishinan ya ce kimanin ‘yan Boko Haram dubu ashirin ne suka mika wuya, dan haka dan mutum shida sun gudu cikin wannan adadi ai ba wani abin ta da kura ba ne, sannan ya ce ba su gudu da makaman da gwamnati ta ba su ba.

Leave a Reply