Guguwar Milton ta sauƙa a jihar Florida

0
51
Guguwar Milton ta sauƙa a jihar Florida

Guguwar Milton ta sauƙa a jihar Florida

Guguwar Milton ta afka wa gaɓar tekun Gulf ta Florida a kudu da Tampa a daren Laraba, tana lalata wutar lantarki tare da zubar da ruwan sama kamar da bakin kwarya, iska mai ƙarfi da ambaliya mai barazana ga rayuwa a sassa na tsakiya da kudu maso yammacin Florida.

Lokacin da guguwar ta sauƙa a kusa da Siesta Key a karamar hukumar Sarasota, Milton tana a matsayin guguwa mai matakin 3 tare da iskar da ke gudun 205 kph (120 mph), in ji Cibiyar Kula da Guguwa ta Ƙasa da ke Miami.

Idon guguwar ta Milton ya afka kilomita 108 kudu da Tampa, amma guguwar ta kawo ambaliyar ruwa – ruwan da ya shiga daga bakin teku zuwa cikin yankunan ƙasa – zuwa biranen Tampa, St. Petersburg, Sarasota da Fort Myers.

An yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliya a daren Laraba ga kusan dukkan gabar yammacin yankin Florida, wanda ya kai tsawon kilomita 500.

KU KUMA KARANTA: Amurka, Kanada za su fuskanci mahaukaciyar guguwa

Fiye da mutum miliyan 1 da kamfanoni suka rasa wutar lantarki, musamman a ƙananan hukumomin Sarasota da Manatee, in ji kamfanin dillancin labarai na Associated Press.

Hukumar ta fitar da fiye da gargaɗi 50 na guguwar iska har zuwa ranar Laraba rana.

Leave a Reply