No menu items!

Sample Page Title

Date:

Mun shirya mayar da martani kan duk harin da aka kawo mana – Iran

Ƙasar Iran ta gargaɗi Isra’ila cewa muddin ta kuskura ta yi gangancin kawo mata hari, to za ta yaba wa aya zaƙi.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi wa Isra’ila jan kunnen ne da cewa kada ta kuskura ta kai haƙurinta bango.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, a cikin wata sanarwar, ya ce, “a yayin da Isra’ila ke gigin rama hare-haren da Iran ta kai mata a makon jiya, ta kwana da sanin cewa makaman Iran masu linzami za su iya isa duk inda aka harba su.

“Kuma mun riga mun shirya mu mayar da martani kan duk harin da aka kawo mana,” in ji Minista Araghchi.

KU KUMA KARANTA: Ƙasar Iran ta karrama kwamandan da ya kai wa Isra’ila hari

Ya jaddada cewa Iran za ta ci gaba da goyon baya da kuma taimaka wa ƙungiyar Hamas da Hizbullah da duk wani yunƙurin ganin Falasɗinawa sun samu ƙasarsu mai cikekken ’yanci.

Da yake jawabi kan kisan shugaban Hizbullah, Sayyid Hassan Nasrallah da Isra’ila ta yi, ministan ya bayyana cewa fito-na-fito da Iran ke yi da Isra’ila ba kan mutum ɗaya ba ne kawai.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...