No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnatin tarayya ta ba da kwangilar fara gyaran titin Abuja zuwa Tafa

Gwamnatin Tarayya ta ba da kwangilar gyaran (faci) wani ɓangare na titin Abuja zuwa Kaduna a kan Naira miliyan 366.

Ma’aikatar Ayyuka ta Ƙasa ta ce za a kashe Naira miliyan kan366 ne wajen yin faci da kuma gyara wuraren da suka lalace a titin daga Zuba da ke Babban Birnin Tarayya zuwa Ƙaramar Hukumar Tada da ke Jihar Neja.

Aikin mai tsawon kilomita 31 zai tsaya ne Mahaɗar Dikko Junction da ke iyakar Jihar Neja da Kaduna, kuma ana sa ran kammala shi cikin makonni biyu.

Kamfanin da aka ba wa aikin facin titin, H&M Nigeria Limited, ya riga ya kai kayansa wurin tun ranar Laraba 2 ga watan Oktoba, 2024.

KU KUMA KARANTA: Najeriya ta samu tallafin dala biliyan 1.3 Don ƙarasa hanyar jirgin ƙasa daga Kano zuwa Nijar

A yayin ziyarar gani da ido da suka kai wajen, Daraktan Kula da Manyan Hanyoyin Yankin Arewa ta Tsakiya, Injiniya Mohammed Goni da takwaransa mai kula da ayyuka na musamman a yakin Arewa, Injiniya Olufemi Adetunji, sun buƙaci kamfanin ya tabbatar ya aiwatar da aikin gyaran, yadda aka tsara kuma a cikin lokaci.

Injiniya Goni ya ba da tabbacin cewa da zarar an kammala aikin, za a ba da kwangilar gyaran ɓangaren da aya tashi daga Tafa zuwa Kaduna.

Yanzu shekara shida ke nan kamfanin Julius Berger ke aikin gyaran babban titin Abuja zuwa Kaduna, ba tare da ya kammala ba.

Yanayin lalacewa da ramukan da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna mai tsawon kilomita 180 ya mayar da hanyar tamkar tarkon mutuwa ga matafiya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...