Gidauniyar JFES ta kai tallafin takardu makarantar Hafsatu Gimba Ahmed Memorial (Hotuna)

0
235
Gidauniyar JFES ta kai tallafin takardu makarantar Hafsatu Gimba Ahmed Memorial (Hotuna)
Ɗaliban makarantar Hafsatu Gimba Ahmed Memorial, Potiskum

Gidauniyar JFES ta kai tallafin takardu makarantar Hafsatu Gimba Ahmed Memorial (Hotuna)

Daga Ibraheem El-Tafseer

A safiyar ranar juma’a da ta gabata ne, gidauniyar ‘Joda Foundation for Education Support’ (JFES) ta kai tallafin takardu makarantar Hafsatu Gimba Ahmed Memorial Potiskum.

Kodinetan makarantar, Malam Ba’aba Ahmed Gimba, shi ne ya yi jawabin maraba da baƙi. A cikin jawabinsa ya fara ne da godewa wannan gidauniya, inda ya ce “muna godiya ga wannan gidauniya bisa ga karamci da suka nuna mana, yadda suka zaɓi wannan makaranta don su bawa ɗalibanmu tallafin takardu. Kune na farko da kuka fara kawo mana tallafin takardu, tun da aka buɗe wannan makaranta” inji shi

Malam Hassan B. Joda yana miƙa takardu ga Kodinetan makarantar, Malam Ba’aba Ahmed

Shi ma a nasa jawabin, Dakta Abdullahi Mamuda, ya jinjina wa wannan gidauniya ta JFES, bisa ga namijin ƙoƙarin da suke yi don ganin yara sun samu ilimi mai inganci haɗe da koyar da dabarun koyon sana’a.

Shugaban JFES FOUNDATION, Malam Hassan Bomoi Joda, ya bayyana wa manema labarai dalilinsa na zaɓar wannan makaranta don tallafawa da takardu.

KU KUMA KARANTA:Makarantar ‘Hafsatu Gimba Ahmed Memorial’ an fara sayar da fom

Ya ce “babban abin da ya ja hankali na, muka ƙirƙiri wannan gidauniya shi ne, irin yawan adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a wannan yanki namu. Akwai yara da yawa waɗanda ba sa zuwa makaranta.

Bayan ƙirƙirar wannan gidauniya a wata shida da ya gabata, abu na farko da muka fara yi, shi ne mun saka yara 16 a makaranta. Sannan muna bi makarantu, muna raba musu kayan karatu, lokaci bayan lokaci.

A wannan karon, abin da ya sa muka zaɓi wannan makaranta shi ne, irin tsarin da makarantar take da shi na koyarwa haɗe da koyar da dabarun koyon sana’ar hanu” inji Joda.

Malam Ba’aba Ahmed Gimba, Kodineta HGA Memorial
Dakta Abdullahi Mamuda
Hira da ɗaliban makarantar
Hira da ɗaliban makarantar
M. Hassan B Joda yana hira da manema labarai
Malam Muhammad Ibrahim Jaji, Hedimasta

Hedimastan makarantar, Malam Muhammad Ibrahim Jaji, shi ma godiya ya yi wa gidauniyar bisa ga ƙoƙari da suke na ƙara wa yara ƙumaji don jin daɗin ci gaba da karatu.

A ƙarshe, sai suka ɗauki hotuna tare da ɗaliban makarantar.

Leave a Reply