No menu items!

Sample Page Title

Date:

Dalilin da ya sa aka kori Seaman Abbas daga aiki — Rundunar Soji

Rundunar tsaro ta ƙasa a Najeriya, ta yi ƙarin bayani game da dalilan sallamar sojan ruwan nan Seaman Abbas Haruna daga aiki.

A wajen wani taron manema labarai da ta ƙira a Abuja, Hedikwatar tsaron ta ce an sallami Seaman Abbas daga aiki ne bayan wata kotun soji ta same shi da wasu laifuka uku da ake zarginsa da aikatawa.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar tsaron ta Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya shaida wa BBC cewa, Seaman Abbas, ya yi wasu abubuwa na rashin ɗa’a.

Abubuwan sun haɗa da ƙin bin umarnin kwamandan bataliya da kuma yin surutu a lokacin da kwamandan ke jawabi ga sojoji.

A cewar Gusau, da kwamandan ya umarci Abbas ya kai kansa wani ɗaki da ake tsare mutane idan sun yi laifi sakamakon kaifin da ya yi, to sai yaƙi zuwa.

KU KUMA KARANTA:Rundunar Sojin Najeriya sun sallami Seaman Abbas da aka tsare tsawon shekaru 6

“Daga nan ne sai kwamandan ya ce tun da yaƙi zuwa to a karɓe bindigar dake hannunsa, to maimakon ya miƙa bindigar sai ya fara harbe-harbe har sai da fitar da harsashi 16, to Allah ya kiyayye bai harbi kowa ba”.

Tukur Gusau, ya ce a ɓangaren aikin soja ba a wasa da batun bindiga ko harsashi, domin harsashi ɗaya idan soja ya fitar sai an bibiya an ga me yasa ka fitar da shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron ta Najeriya, ya ce, “Bisa ga wannan aka tuhumeshi inda aka tura shi kotun soja kuma koda aka kai shi ya amsa laifinsa, a kan haka ne kotu ta tuhumeshi da aikata laifuka uku”.

Ya ce a watan Fabrairun 2023, kotun ta kore shi daga aiki.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...